1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Rome a game da Labanon

Yahouza Sadissou MadobiJuly 26, 2006

An kammala taron yini ɗaya a birnin Rome na ƙasar Italia a game da yaƙi tsakanin Isra´ila da Hezbollah.

https://p.dw.com/p/Btys
Hoto: AP

An kammala taron birnin Rome na ƙasar Italia, a game da yaƙi tsakanin Hezollah da Isra´ila.

An kiri taron bisa gayyatar Majalisar Ɗinkin Dunia a yunkurin da ta ke na tsagaita wutar yaƙe- yaƙe tsakanin Isra´ila da Hezbollah wanda a yau, ya shiga yau kwana na 15.

Taron na birnin Rome, ya samu halartar ƙasashen 15, da manyan ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa guda 3.

Kamin a fara mahaurori, saida mahalatan su ka yi tsayuwar shuru,ta minti 1, a matasayin addu´a ga wanda su ka rasa rayukan a cinkin yaƙin.

A yayin da ya gabatar da jawabi, praminsitan Lababan Fouad Siniora, ya bayana shigar da ƙaran Isra´ila a dalilin ɗimbin assara dukiyoyi da rayuka, da ta hadasa cikin ƙasar Labaon

Fouad Siniora ya bayana hanyoyin guda 7, wanda a cewar sa, za su iya samar da tsagaita wuta.

Na farko ya bukaci yin masanyar prisinonin yaƙi tsakanin ɓangarorin 2, bisa jagorancin hukumar Red Cross.

Kuma dakarun Isra´ila sun janye daga yankuna ƙasar Labanon da su ka mamaye

Majalisar Ɗinkin Dunia, ta aika rundunar ta, a yankuna Sheeba, ta kuma ƙara ƙarfafa dakarun ta da ke Labanon.

Sannan wajibi ne gwamnatin Labanon ta kulla, da faɗin kasa ta saɓanin yanzu, da yan Hezbollah ke riƙe da wani yanki.

Bayan yini 1 a na tabka mahaurori, mahalarta taron Rome ,sun hido sanarwar ƙarshen taro, wace ta tanadi aika rundunar shiga tsakanin ta Majlisar Ɗinkin Dunia tare da yi mata guzurin makamai da kayan aikin da su cencenta.

Mahalarta taron sun gayyaci Isra´ila da Hezbollah su tsagaita wuta cikin gaggawa.

Sakatariyar harakokin wajen Amurika Condoleesa Rice, da ta jagorancin taron tare da takwaran ta na Italia, tayi taron manema labarai domin bayana matsayin da su ka cimma.

Ta ce baki ɗaya mun amince da samar da kwaciyar hankali mai ɗorewa.

Saidai abin takaici ne, kasancewa yankin na fuskantar tunƙa da warwara, a sabili da tsofin balshen rigingimu.

Mun sa cewar ƙasashen dunia, sun yi alƙawura ga ƙasar Labanaon, ta hanyar ayar dokar mai lamba 1559, wace Majalisar Ɗinkin Dunia, ta tanada, domin taimakawa ƙasar Labanon, ta samu zaman lahia, ba tare da katsalandan ba, na ƙasashe maƙwabtan ta, amma haƙa ta kasa cimma ruwa.

Shima sakatare Jannar na Majlaisar Dinkin Dunai Koffi ya huruci jim kaɗan bayan kammalla taro.

Ya ce :“da zaran mu ka tashi da wanna taro ya na da mahimmanci mu ci gaba da faɗi ka tsahi na nemo hanayoyin tabbatar da zaman lahia a wannan yanki.

Wajibi ne mu samu wata babbar madogara da zata kasance garkuwa, ga ƙiƙƙi-ƙaƙƙar da kan iya ɓullowa a komitin sulhu a lokacin gudanar da mahaura tsakanin ƙasashen da abun ya shafa.

Wajibi ne kuma, mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da ƙasashen yanki domin cimma tudun dafawa, hata da Iran da kuma Syria.

Taron na Rome bai samu wakilci ba, daga ɓangaren Isra´ila ko na Hezbollah, a halin yanzu jama´ar Labonon sun zuba ido, su ga ko zahiri Majalisar Ɗinkin Dunia da ƙasashen da su tura wakilai, za su cika alkawuran da su ka ɗauka.