1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron SADC a birnin Lusaka

August 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuDw

Ƙasar Zimbabwe ta jaddada yin watsi da kiran da ƙasashen dunia ke mata, na gudanar da cenje cenje ga harakokin mulki.

Shugaban ƙasa Robert Mugabe, ya bayyana haka albarakacin bikin buɗe taron ƙungiyar haɗa kann ƙasashe 14, na yankin kudancin Afrika ,da aka yi jiya, a birnin Lusaka na kasar Zambia.

A yayin da ya ke hira da yan jarida a game da wannan batu, ministan shari´a Zimbabwe Patrick Chinamasa, ya nunar da cewa batun gudanar da kwaskwarima bai taso ba, a harakokin mulkin Zimbabwe, domin ƙasar na bin tafarkin demokrirdiya kamar sauran ƙasashen dunia.

A nasa ɓangare shugaba mai masaukin baƙi, Levy Mwanawasa, ya yi kira ga yan ƙasar Zimbabwe, su duƙufa wajen samar da zaman lahia, da kuma masalaha a game da harakokin siyasa.

taron na birnin Lusaka da za a kamalla yau, ya maida hankali kusan baki ɗaya a game da halin da ake ciki a ƙasar Zimbabwe, ta fannin harakokin siyasa da kuma tattalin arziki.