1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sasanta alúmomin ƙasar Lebanon

July 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuGR

Jamiíyun adawa na ƙasar Lebanon a yau sun fara wani taron yini biyua Faransa a ƙoƙarin warware taƙaddamar dake tsakanin su wanda yake neman durƙusar da ƙasar. A waje guda dai yayin da aka buɗe wannan tattaunawa, sojojin ƙasar ta Lebanon na can na fafatawa da yan kishin Islama a sansanin yan gudun hijira na Nahr al-Bared dake arewacin Lebanon. Kusan dai wakilan dukkan ƙungiyoyin siyasa 14 na ƙasar Lebanon sun halarci taron ciki kuwa har da wakilan gwamnatin ta P/M Fuad Siniora mai samun goyon baya daga yammacin turai, bugu da ƙari da kuma yan ƙungiyar Islama ta Hizbullah. Ƙasar Faransa ta jima tana ƙoƙarin jagorantar sasantawar da ake fatan zata kawo daidaituwar alámura a ƙasar Lebanon. A yanzu dai Faransan na da sojoji 1,600 waɗanda aka girke a kudancin Lebanon ƙarkashin shirin aikin kiyaye zaman lafiya na majalisar ɗinkin duniya.