1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sasanta al´umar ƙasar Somalia a birnin Mogadishu

July 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuGL
A yau lahadi a birnin Mogadishu ake fara wani babban taron sansanta al´umar kasar Somalia bayan an yi ta dage zaman taron har sau uku. Taron zai kuma tattauna game da makomar kasar ta Somalia wadda yaki yayiwa kaca-kaca. To sai dai masu kishin Islama sun yi barazanar katse taron saboda haka dakarun gwamnati dake samun daurin gindin Ethiopia sun tsaurara matakan tsaro a wurin da za´a gudanar da taron. Wakilan kimanin dubu 1 da 300 ciki har da shugabannin kabilu, tsofaffin madugan yaki da kuma ´yan siyasa ake sa rai zasu halarci wajen taron. Manazarta al´umar yau da kullum na ganin taron a matsayin wata dama ta karshe ga shugaban rikon kwarya Abdullahi Yusuf na ya samar da zaman lafiya mai dorewa a Somalia. A karshen shekara ta 2006 dakarun Ethiopia suka taimaka aka fatattaki sojojin sa kai na kotunan Islama daga birnin Mogadishu, to sai dai har yanzu ana ci-gaba da dauki ba dadi a babban birnin na Somalia.