1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sasanta ´yan Iraki a birnin Alkahira

Mohammad Nasiru AwalNovember 21, 2005

Taron ya amince da shirya taron kasa baki daya a Iraki a cikin watan fabrairu mai zuwa.

https://p.dw.com/p/Bu43
Shugaba Jalal Talabani
Shugaba Jalal TalabaniHoto: AP

An dai amince cewar a cikin watan fabrairu za´a gudanar da babban taron sasanta al´umar Iraqi. To amma har yanzu ba´a bayyana wadanda zasu halarci taron ba. Muhimmin batun da ya zama wajibi a warware shi gabanin wannan taro dai shi ne bambamcin tsakanin gwagwarmaya da makami da ta´addanci.

Tun dai watanni da dama da suka wuce Iraqi ta zama wani dandalin kai munanan hare hare babu kakkautawa musamman ma a lokacin wannan taro na yini 3 da aka kammala yau litinin a birnin Alkahira. Wadannan hare haren dai tamkar wani sako ne da masu ta da kayar bayan ke aikewa cewa ba zasu yarda a raba da su da ´yancin yakar wadanda suka kira abokan gaba ba.

Wadannan nan abokan gaban ga ´yan sunni kuma ´yan tawaye su ne sojojin Amirka da kawanyensu da suka mamaye Iraqi da duk masu ba su hadin kai wato kamar ´yan shi´a da kurdawa.

Sabanin matsayin sa gabanin taron, a jiya lahadi shugaban Iraqi Jalal Talabani ya ce a shirye ya ke ya tattauna da masu gwagwarmaya da makami muddin suka ajiye makaman su.

„Ina lale maraba da duk mai daukar kansa a matsayin dan tawaye a Iraqi amma ya nuna shirin ganawa da ni.“

Dole ne Talabani ya nuna cewa da gaske ya ke a wannan tayi na tattaunawa da ´yan tawaye, muddin ana son a mayar da masu tsattsauran ra´ayin nuna adawar saniyar ware, inji Mohammed El-Faidi kakakin majalisar limaman ´yan sunni a Iraqi.

„Ba zamu iya yin watsi da masu ta da kayar bayan ba. Dole ne mu tattauna da su da nufin kawo karshen tashe tashen hankulan da suka zama ruwan dare a cikin kasar.“

Su dai ´yan sunni na fargabar cewa ana iya mayar da su saniyar ware a cikin sabuwar gwamnatin Iraqi. Suna korafi game da yawan tasirin da ´yan shi´a ke samu a cikin kasar da fatattakar ´yan sunni da gwamnatin da ´yan shi´a din suka yiwa babakere ke yi. Musamman bayan gano wani gidan yare dake karkashin ginin ma´aikatar cikin gida cikin makon jiya.

Yanzu haka dai kungiyar kasashen Larabawa na kokarin yin sulhu. To amma Kurdawa da ´yan shi´a na nuna shakku da haka musamman ganin cewa ´yan sunni ne suka fi rinjaye a cikin kungiyar. Baya ga haka kuma kungiyar ta ki fitowa karara ta yi tir da ´yan sunni masu ta da kayar baya a Iraqi.

A karshen watan fabrairu na shekara mai zuwa ake sa ran gudanar da taron sulhun. Kafin wannan lokaci kuwa za´a ci-gaba da cecekuce akan wadanda suka cancanci shiga wannan taro.