1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Merkel na ganawa da shugabbin EU

Lateefa Mustapha Ja'afar
June 24, 2018

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugabannin kasashen kungiyar EU 15 na gudanar da wani kwarya-kwaryar taro a birnin Brussels na kasar Beljiyam.

https://p.dw.com/p/30C2z
EU-Minigipfel
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da takwarorinta na EUHoto: picture alliance/AP Photo/Y. Herman

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugabannin kasashen kungiyar EU 15 na gudanar da wani taron gaggawa kan matsalar 'yan gudun hijira a Brussels, a wani mataki na share fagen taron da za su gudanar a ranakun 28 zuwa 29 ga wannan wata na Yuli da muke ciki domin samo mafiota kan matsalar ta 'yan gudun hijira da ke neman wargaza gwamnatin hadaka ta Jamus. Merkel da ke zaman shugabar jam'iyyar CDU na fuskantar matsalin lamba daga ministan cikin gida Horst Seehofer kana shugaban jam'iyyar CSU da ke zaman abokiyar tagwaitakar jam'iyyar Merkel din, a kan batun bakin haure da masu neman mafaka.