1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron share fage na taron kolin tattalin arzikin duniya a Rasha

June 9, 2006
https://p.dw.com/p/Buuj

Ministocin kudi na kungiyar kasashe 7 da suka fi arzikin masana´antu a duniya da kuma Rasha, wato G8 sun isa a birnin St. Petersburg inda zasu gudanar da taron share fagen taron koli kan tattalin arzikin duniya da za´a yi tsakiyar watan yuli. Yanzu haka dai ministan kudin tarayyar Jamus Peer Steinbrück ya tattauna ta bayan fage da takwarorinsa na kasashen Amirka da Rasha wato John Snow da kuma Alexey Kudrin. Hakazalika ministan ya kuma gana da shugaban asusun ba da lamuni na dunyia IMF, Rodrigo Rato a yau juma´a. Muhimmin batun da zai fi daukar hankali a taron ministocin kudin da zai gudana gobe asabar shi ne game da samar da makamashi a duniya.