1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shawo kan matsalar bakin haure a Libya

Zainab A MohammadNovember 21, 2006

A gobe laraba ne wakilan kasashen Afrika dana turai dake kokarin shawo kann matsalar bakin haure dake fitowa daga Afrika zuwa turai din,zasu bude wani muhimmin taro na nazarin wannan Lamari a birnin Tripolin kasar Libya.

https://p.dw.com/p/BtxM

Taron hadin gwiwan tsakanin kasashen turai dana nahiyar Afrika dake zama na farkon irinsa akan matsalar bakin haure,nada nufin nunar dacewa sassan biyu zasu iya hada kafada da kafada domin aiki tare ,wajen karfafa dangantar tsaro a kann iyakokin su,walau ta cikin teku ko kuma sauran hanyoyin da bakin hauren kebi.Yin hakan ne kuwa zai rage damar da bakin hauren ke dasu na bin shiga nahiyar turai ta arewacin Afrika.

To sai manazarta na ganin ababaikaslilan ne zaa iya cimma a wannan taro na yini biyu,dayake babu batun alkawrin bada kudin gudanar da wannan aiki.

Amadadin haka Taron zaiyi nazari ne dangane da matakai da zaa hanga na taimakawa shawo kann kujewa nahiyar Afrika da yayanta keyi,ta hanyar samar musu da aikin yi a kasashensu na haihuwa.

Sanarwar data fito daga kungiyar tarayyar Afrika Au,na jaddada bukatar kawo karshen wannan mummunan yanayi ,wanda ke dada haifar da nuna banbanci da wariya da kiyayya da bacin rai.

Ita kuwa mataimakiyar babban Directa a maaikatar harkokin wajen kasar Finland,wadda itace kasar dake shugabantar EU, Anne Sipilainen,cewa tayi baa sanya ran samun sakamakon wannan taro cikin gaggawa.Amadadin haka ta bayyana cewa taron na yini biyu,taro ne na siyasa domin bangarorin biyu su aike da sakon cewa zasu iya hadin kai domin aiki tare.

Madam Anne tace taron zaiyi nazarin muhimman batutuwa da suka hadar da zaman lafiya da tsaro da yancin jamaa da matsaloli na kwararan yan Afrika masu ilimi zuwa turai saboda rashin ingantaccen rayuwa a kasashensu na asali,ta inganta cigaba.

Gididdiga na nuni dacewa a wannan shekara kadai akwai yan Afrika kimanin dubu 26,mafi yawansu yan kasar Senegal,dasuka bi barauniyar hanyar nan ta tsibirin kasar Spain,akokarinsu na shiga turai.Ayayinda dubban wasu sun cimma nasaran shiga turan ta kasashen Morokko da Libya,bayan sun keta sahara.

Kasashen turan dai suna cigaba da zargin takwarorinsu na Afrika dayin watsi da yarjejeniyar da aka cimma na shawo kann yawan kwararan bakin haure.ayayinda su kuma gwamnatocin Afrika suke muradin dada rage matsin lamba da akewa wadanda ke shiga turan a hukumance,tare da samarda taimakon raya kasashen.A kowace shekara dai an kiyasta cewa yan Afrika dubu 200 ke shiga turai ta barauniyar hanya,ayayinda ake cafke wasu dubu 100.