1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shinfiɗa zaman lahia a ƙasar Labanon

March 4, 2006
https://p.dw.com/p/Bv64

Jam´iyun siyasa, da ƙungiyoyi daban-daban na ƙasar Labanon, sun shiga kwana na 3, a taron da suka shirya, domin neman mattakan samar da zaman lahia a wannan ƙasa.

Bayan cimma daidaito, a kan matakin girka kotun ƙasa da ƙasa, domin gudanar da shari´a ga masu alhakin kashe tsofan Praminista Raffik Hariri, mahalarta wannan taro, da su ka haɗa da shugabanin musulmi da na kristoci, sun fara masayanr ra´ayoyi, a game da batu mai sarƙaƙiya, na kwance ɗamara yaki ga ƙungiyar Hezbollah, da kuma, matsayin shugaban ƙasa Emil Lahud, da wasu ke zargi da zama karan farautar Syria.

Sannan za su tanatana batun hulɗoɗi tsakanin Labaon da Syria, wanda a baya bayan nan, su ka fuskanci tabarbarewa.

A na shirya wannan taro, tare da taimakon Bankin Dunia, da Amurika, da kungiyar gamayya turai, da sauran ƙasashen larabawa na yankin tekun Pasha.

Gobe lahadi ne,idan Allah ya kai mu, ake sa ran kawo ƙarshen taron.