1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabanin ƙasashen ƙungiyar ECOWAS a birnin Abuja.

June 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuIj

Shugabanin ƙasashen ƙungiyar haɓɓaka tattalin arzikin yankin yammacin Afrika, wato ECOWAS kokuma CEDEAO, sun fara taron ƙoli a birnin Abuja na Tarayya Nigeria, bisa jagorancin shugaban ƙungiyar, Blaise Campaore na Burkina Faso.

Mahimman batun da su ke tabka mahaurori kann sa, ya jiɓanci mu´amilar cinikaya, da cuɗe ni in cuɗe ka, tsakanin ƙashashe 16 membobin wannan ƙungiya

Tun shekara ta 2002, ƙasashen ECOWAS su ka alƙawarta shinfiɗa matakin yaye shige, ta fannin saye da sayarwa tsakanin su, to saidai ya zuwa yanzu, wannan mataki ya kasa aikatuwa a zahiri.

Shugabanin za su anfani da wannan dama, domin bitar halin da ake ciki a kan batun tare da zayyana sabin hanyoyin cimma burin da aka sa gaba..

A ɗaya hannun shugabanin ECOWAS, za su maida hankali a kann matsalar baƙin haure, da ke kwarara turai, daga yammacin Afrika.

Nan gaba a yau, za a kammala wannan taro, tare da bayyana sakamakon da ya cimma.