1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabanin adawa da na yan tawaye a Cote d´Ivoire

August 17, 2006
https://p.dw.com/p/BumQ

Nan gaba a yau ne,shugabanin jam´iyun adawa, da yan tawayen Cote d´Ivoire za su tantana, a birnin Daoukro da ke gabas maso tsakiyar ƙasa.

Shugaban jam´iyar PDCI, bugu da ƙari tsofan shugaban ƙasa Henri Konnan Bedie, da shugaban jam´iyar RDR Allasane Watara, da kuma Guillaume Soro, madugun yan tawaye, za su masanyar ra´ayoyi, a game da dambarwar siyasar da ke wakana a wannan ƙasa.

Tun farkon watan da mu ke ciki, al´mmura su daɗa rincaɓewa a Cote d´Ivoire, bayan kalamomin shugaba Lauran Bagbo, na cewar zai ci gaba, da kasancewa kan karagar mulki, bayan ranar 31 ga watan Oktober wato ƙarshen wa´adin da, Majalisar Dinkin Dunia ta yanke masa, a shekara da ta gabata.