1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabanin kasashen Euromed a Barcelona na Spain

November 28, 2005
https://p.dw.com/p/BvJ3

Shugabanin kasashen da ke gabobin tekun Medetiranne, sun buda zaman taro na farko a birnin Barcelona, na kasar Spain.

Kasashen sun hada da na turai, da na yankin larabawa dake karbun kudu da arewancin wannan teku.

An girka kungiyar hadin kan kasashen tun shekara ta 1995.

Mahuiman batutuwan da mahalarta wannan ke cikin tantana wa a kai, sun hada da yaki da ta´adanci da kuma matsalar bakin haure, da ke kwarara daga gabar kudu zuwa gabar arewa, ta kogin Mediteranne.

Saidai daga shugabanin kasashen yankunan larabawa 10 membobin kungiyar 2 rak su ka halarci taron wato shugaban hukumar Palestinawa Mahamud Abbas, da kuma Praministan Turkiyya Recep Tayyip Erdowan.

Taron da ke gudana bisa jagorancin Pramistan Spain Jose Luis Rodrigez Zapatero mai masabkin baki, da Tony Blair na Britaniyya, bugu da kari shugaban kungiyar gammayya turai zai kawo karshe nan gaba a yau

Shugabar gwamnatain Jamus Angeller Merkel da ke halartar taron, ta yi anfani da wannan dama inda ta tantana da Tayyib Erdogan na Turkiyya.

Har ma ta amsa gayyatar da yayi mata, na zuwa ziyara a kasar Turkiyya.