1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabannin duniya a New York

September 24, 2010

Wakilan ƙasashen yamma a taron MƊD dake gudana a birnin New York sun fusata, bisa kalaman shugaba Ahmadijad, inda yace Amirka ce ta kitsa harin sha ɗaya ga watan satumba 2001

https://p.dw.com/p/PLVz
Mahmoud AhmadinejadHoto: AP

Shugaban ƙasar Amirka Barack Obama ya yi ƙira ga shugabanni duniya da su kawo duk gudumawar da za su iya, don tabbatar da zaman lafiya ya samu tsakanin Yahudawa da Palasɗinawa. Da ya ke jawabi a taron babban tsauren MƊD inda shugabannin duniya suka hallara, Obama yace dole ne a gaggauta yin aiki tare, don samar da ƙasar Palasɗinu mai 'yancin kanta da kuma ƙasar Isra'ila dake da cikakken tsaro a nan da shekara guda. Bayan jawabin nasa sai shugaba Ahmadinajad ya shigo ya fara na shi jawabin, da ya fara caccakan ƙasashen yamma, sai waklilin Amirka dana Birtaniya da Faransa da na wasu ƙasashen suka pice daga taron a fusace. Daga cikin kalaman Ahmadinajad da suka fusatar da wakilan ƙasashen yammaci, sun haɗa yadda shugaban ƙasar ta Iran ya fito ƙarara yace Amirka ce da kanta ta kitsa harin sha ɗaya ga watan satumba wanda aka kaiwa cibiyar kasuwanci ta duniya da kuma helkwatar tsaro ta Pentagon, domin kwai ta ƙarfafa kan kane al'amura a gabas ta tsakiya da kuma dai-daita tattalin arzikin ta.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu