1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

220209 G20 Berlin

Mohammad AwalFebruary 23, 2009

Shugabannin ƙasashen Turai mafiya ƙarfin tattalin arziki sun amince da ƙirƙiro wani nagartaccen tsarin tafiyar da harkokin kuɗi a duniya.

https://p.dw.com/p/GzjL
Mahalarta taron ƙolin shugabannin EU a BerlinHoto: AP

Yayin da jiya a wasu yankunan Jamus batun bukin Karnival ya ɗauki hankali, a birnin Berlin kuwa ba a san ana wannan buki ba domin shugabar gwamnati Angela Merkel ta gayyaci shugabannin ƙasashen Turai mafiya ƙarfin tattalin arziki zuwa wani taron share fage gabanin taron ƙolin ƙungiyar G20 da zai gudana a London a farkon watan Afrilu. A taron na Berlin shugabannin na Turai sun tattauna game da ƙirƙiro wani sabo tsarin tafiyar da kasuwannin kuɗi.

A lokacin taron dai ba a samu yanayin sararin samaniya mai kyau ba a birnin na Berlin, abin da yayi kama da mawuyacin halin da kasuwannin kuɗi da tattalin arziki ke ciki. Tun bayan taron ƙoli kan harkokin kuɗi na farko tsakanin ƙasashe masu arzikin masana´antu da masu tasowa da ya gudana a birnin Washington cikin watan Nuwamban bara abubuwa sai ƙara taɓarɓarewa suke yi. Ƙasashen ƙungiyar G20 da takwarorinsu na Turai guda shida na cikin wani matsatsi. Bayan taron a fadar gwamnatin Jamus an jiyo shugabar gwamnati Angela Merkel tana mai cewa bai kamata a sake fuskantar irin wannan matsala ba.

"Mun san cewa dole ne dukkan kasuwannin hada-hadar kuɗi da na hananyen jari da kuma dukkan dillalai su kasance ƙarƙashin sa idon wata hukuma tare da bin dokoki da aka zayyana. Za mu sake yin nazari kan abubuwan da wannan shiri ya ƙunsa."

Tun a taron ƙolin G20 a Washington aka amince da wannan shiri wanda yaƙunshi rukunai 47 kuma yanzu aka sanya shi ƙarƙashin wasu ƙungiyoyin ƙwararru huɗu. Sabon abu a nan shi ne haɗin kan da aka samu tsakanin Turawan abin da ba a gani ba a Washington. Domin yanzu ƙasashen Turan su ƙuduri aniyar jan kunnen duk wanda ya ƙi ba da haɗin kai ga wata cibiyar musayar bayanai game da kuɗaɗen haraji, kamar yadda shugaban Faransa Nikolas Sarkozy ya nunar.

"Dukkan mu ƙuduri aniyar ganin cewa taron da za mu yi London yayi nasara kasancewarsa wata dama ta ƙarshe a garemu. Nahiyar Turai na son a sakewa tsarin tafiyar da harkokin kuɗi fasali gaba ki ɗaya. Kuma dukkan mu mun amince da haka."

Ita ma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tun a gun taron tattalin arzikin duniya a garin Davos ta nuna amincewa da shawarar kafa wani tsari da zai tabbatar da ɗorewar bunƙasar tattalin arziki. Wannan tsari ya haɗa da daidata kasuwanni da kuma nuna halin sanin ya kamata da kuma ɗaukar matakan yaƙi da manufar nan ta kare masana´antun ƙasa ta hanyar ƙara kuɗaɗen haraji ga kayan da ake shiga da su wannan ƙasa daga ƙetare. A nasa ɓangaren firaministan Birtaniya Gordon Brown ya yi magana game da wani sabon shiri a tsarin tattalin arzikin duniya baki ɗaya.

"Mun ga wani shirin tallafawa tattalin arziki mafi girma da aka yi a duniya wato kamar rage yawan kuɗin ruwa. Kuma yanzu mun ga yadda ake tura maƙudan kuɗaɗe cikin tsarin bankunanmu don ba su damar sake ba da bashi. To sai dai da sauran rina a kaba wajen tabbatar da samun cikakken haɗin kai tsakanin ƙasashen duniya. Muna buƙatar nagartattun matakan don samun wani ginshiƙin tattalin arziki mai ma´ana kuma mafi ƙarfi."

Brown ya jaddada cewa za´a ci-gaba da aiwatar da waɗannan matakan domin ganin sun ɗore.

Kinkartz, Sabine

Fassara: Mohammad Nasiru Awal