1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhu na shugabannin musulmi da yahudawa a Spaniya

March 20, 2006
https://p.dw.com/p/Bv4Y

Shugabannin musulmi da yahudawa sun bude wani babban taro yau a kasar Spaniya,tare da nufin sulhu tsakanin addinan biyu,inda sukayi gargadin cewa taaddanci na addini yana daya daga cikin manyan kalubale da duniya take fuskanta a yanzu.

Rabbi Israel Singer,shugaban kungiyar yahudawa na duniya wajen bude taron na kwanaki 4 da wata kungiyar tabbatar da zaman lafiya dake Paris ta shirya yace taron zai taimaka kwarai wajen kare masifa ko mummunan tashe tashen hankula na addini.

Yarima Hassan na Jordan,danuwan sarki Abdalla cikin sakonsa ga taron yace akwai bukatar musulmi da yahudawa suyi aiki tukuru wajen fahimtar junansu.

Yace ana bukatar sake komawa ga littafai masu tsarki na addinan biyu domin kara fahimtar juna.