1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhu tsakanin yan tawayen LRA da gwamnatin Uganda

July 19, 2006
https://p.dw.com/p/Bu69

Masu shiga tsakani daga Uganda sunki amincewa da kiran da kungiyar yan tawaye ta LRA sukayi na tsagaita wuta,a matsayin mataki na farko a tattaunawar gano bakin zaren warware rikicin yan tawaye mafi dadewa a nahiyar Afrika.

Shugaban tawagar masu tattauna daga bangaren gwamnati, kuma ministan harkokin cikin gida Ruhakana Rugungu,ya fadawa taron manema labaru cewa,a baya alokacin da suka bukaci tsagaita wuta,lokacin ne yan tawayen ke dada aza makamai tare da matsa kaimi wajen kai hare hare.Yace batun tsagaita wuta zaizo ne bayan an cimma daidaito akan dukkan muhimman batutuwa.

Batun na tsagaita wuta dai,shine batu na farko a agendojin tattaunawar bangarorin biyu da aka fara gudanarwa ranar lahadi a garin Juba,dake kudancin Sudan dake makwabtaka da Ugandan.gwamnatin yankin kudancin Ugandan dai ta bayyana muradinta na cimma daidaituwa a dangane da wannan rikici daya kashe dubban daruruwan mutane,baya ga sama da million biyu da suka kauracewa matsugunnensu.To sai dai bisa dukkan alamu bangarorin biyu na cigaba da fuskantar takaddama.