1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhun lardin Darfur a ƙasar Libya

October 28, 2007
https://p.dw.com/p/C15V

A garin Sirte na kasar Libya ana ci-gaba da taron neman bakin zaren warware rikicin lardin Darfur dake yammacin kasar Sudan duk kauracewa masa da wasu kungiyoyin ´yan tawaye suka yi. Mahalarta taron na kokarin gano hanyoyin kawo kasreh rikicin na Darfur da aka shafe shekaru 4 ana yi tsakanin ´yan tawaye da sojojin Janjaweed dake samun daurin gindin gwamnati a birnin Khartoum. Andrew Natsios wakilin Amirka na musamman a Sudan ya nunar da cewa rundunar hadin guiwa ta MDD da KTA da ake shirin turawa a Darfur ba zasu iya magance matsalolin lardin su kadai ba.

Natsios:

“Ko da yake dakarun na kasa da kasa zasu yi tasiri amma ba zasu iya magance dukkan matsalolin yankin ba. Ina jin al´umar yankin na ganin cewa za´a samu kwanciyar hankali da zarar dakarun sun isa can, amma ba haka ba ne. Ba su san cewa dole sai an samu wata masalaha ta siyasa kafin dakarun su samu nasara.”