1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhunta rikicin Afrika

June 14, 2007
https://p.dw.com/p/BuIs

Wakilai daga ƙasashe 20 na Afrika, sun kawo ƙarhen taron kwanaki 3, a birnin Kinshasa na Jamhuriya Demokrdaiyar Kongo, a game da batun kwance ɗamara yaƙi a Afrika.

Wannan shine karo na 2, da ƙasashen Afrika su ka shirya irin wannan taro, da zumar cimma matakin warwarewa, ko kuma riga kafi, ga tashe-tashen hankulla da ke ci gaba da ɗaiɗaita nahiyar.

A ranar farko, mahalarta taron, sun yi bitar nasarorin da aka cimma, ko kuma akasin haka, tun bayan taron farko, da ya wakana a birnin Freetown na ƙasar Saleo a shekara ta 2005.

Wakilin musamman na Majalisar Ɗinkin Dunia, William Swing ya bayyanan mahimmancin wanan taro, ta fannin masanyar husa´o´i, tsakanin ƙasashen Afrika da su ka yi nasara ɗinke ɓarakar rikicin tawaye, da wanda ke fama da ita har yanzu.