1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhunta rikicin Cote d`Ivoire

Yahouza S. MadobiFebruary 20, 2007

Tawagogin gwamnati da na yan tawayen Cote d´Ivoire na cigaba da taron sulhu a birnin Ouagadougou.

https://p.dw.com/p/Btw8

A birnin Ouagadougou na Burkina Faso, a na ci gaba da tattanawa tsakanin tawagar gwamnatin Cote d´Ivoire, da yan tawaye, wanda ke riƙe da arewancin ƙasar tun shekara ta 2002.

An fara wannan tattanawa tun makon da ya gabata, bisa jagorancin shugaban ƙasar Burkina Faso Blaise Compaore bugu da ƙari, shugaban Ecowas kokuma CEDEAO, wanda hukumar ta naɗa, a matsayin mai shiga tsakanin rikicin Cote d´Ivoire.

Mataimakin shugaban tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia a Cote d´Ivoire Mallam Abu Musa da ke halartar taron ya hurta cewar akwai mutuƙar ci gaba a masanyar ra´ayoyi da ɓangarorin 2 ke ci gabada yi.

Abu Musa ya bayana gamsuwa agame da haka to saida kamar yadda ya bayyana, har yanzu akwai sauran rina kaba,a kan hanyar warware rikicin ƙasar baki ɗaya.

A saboda haka, bai ƙayyade ranar kammalla wannan taro ba, wanda shine irin sa na barkatai, da gwamnati da kuma yan adawa su ka shirya, ba tare da cimma buri ba.

A lokacin da aka buɗa taron, shugaban tawagar Majalisar Ɗinkin Dunia a Cote d´Ivoire, Pierre Schori, ya yi kira ga yan siyasar ƙasar, su yi wa Allah da annabin sa, su ba maraɗa kunya, ta hanayar cimma daftarin samar da zaman lahia a wannan ƙasa, da ta sami kanta a yanayin tsaka mai wuya, tun shekaru 5 da su ka gabata.

Ya zuwa yanzu, babban batun da ke hana ruwa gudu, a tattanawar, ya jiɓanci kwance makaman yan tawaye, da na ƙungiyoyin sa kai, masu bada goyan baya ga shugaba Lauran Bagbo, sai kuma shirye –shiryen zaɓen gama gari, da a tsara gudanarwa a wannan shekara ta 2007.

Sannan batu na 3, mai sarƙƙaƙiya, shine na rijistan masu kaɗa ƙuri´a, wanda tun yaushe, a ka samu rashin fahintar juna kan sa, tsakanin ɓangarorin 2.

A farkon watan da mu ke ciki, shugaban komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Dunia Peter Burian, ya bayyana damuwa a game da tafiyar hawainiya da ake fuskanta, a yunƙurin samar da zaman lahia a Cote d´Ivoire.

Jami´in diplomatian, ya yi bayani mussamman a kan kon gaba kon baya, da ƙudurin Majalisar Ɗinkin Dunia mai lamba 1721, wanda ya shata hanyoyin tsara zaɓe a Cote D´Ivoire.