1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhunta yan Somalia a birnin Khartum

September 4, 2006
https://p.dw.com/p/Bukh

A birnin Khartum na kasar Sudan, a na ci gaba da tantana wa tsakanin gwamnatin riƙwan ƙwaryar Somalia da dakarun Kotunan musulunci, da ke riƙe da birnin Modadiscio da kuma wasu sassa na ƙasar.

An na shirya wannan haɗuwa, bisa jagorancin ƙungiyar ƙasashen Larabawa.

Gwamnatin riƙwan ƙwarya, ta shawarci kotunan Islama su haɗe da rundunar ƙasa.

A halin da ake cikin tantanawar na fuskantar ƙiƙi-ƙaƙa. Kanun ɓangarorin 2, sun rarrabu ta fannoni da dama. Dakarun kotunan musulunci, sun yi watsi da shawara hadewa da runduna gwamnati,bugu da ƙari, sun zargi gwamnatin, da zama karen farautar Ethiopia.

Kazalika, matsayin ɓangarorin 2, ya banbanta, a kan batu runduna shiga tsakani, ta ƙasa da ƙasa.

Saɓanin Gwamnati, dakarun kotunan Islama, na adawa da karɓar wannan runduna.

Kwana ɗaya kamin fara taron, dakarun kotunan musulunci, sun bukaci samun muƙƙamai a cikin gwamnmatin riƙwan ƙwarya.

Majiyoyin diplomatia a ƙasar Somalia, sun hurta cewar damawa da wakilan kotunan islama a cikin gwamnati, na iya kawo ƙarshen rikicin.