1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sunhunta Somalia a Sudan

Zainab A Mohammed.June 21, 2006
https://p.dw.com/p/Btzg
sojojin sakai a somalia
sojojin sakai a somaliaHoto: AP

Ana saran cewa wakilan gwamnatin rikon kwarya dana hadin gwiwar kungiyoyin musulmi dake adawa a Somalia,zasu halarci taron sulhu,da kungiyar gamayyar larabawa mai shiga tsakani ke jagoranta a birnin kartum,fadar gwamnatin Sudan.

Shugaba Hassan Omar Elbashir na sudan,wanda kuma shike rike da kujerar shugabancin kungiyar gamayyar kasashen larabawan na yanzu ,yace zaiyi kokarin kawo shugaban gwamnatin riko na Somalia Abdullahi Yusuf Ahmed da shugaban sojojin sakai na islama dake adawa Shekh Shariff Ahmed,teburin tattaunawa ,domin rage tashe tashen hankula da somalian ta tsinci kanta ciki.

A halin da ake ciki yanzu haka dai hadin kotunan shariar kasar dake karshin sheikh Ahmed ,na rike da birnin mogadisho da kuma kudancin Somalia,bayan fatattakan shugabannin hauloli da Amurka ke marawa baya ,a fadan watanni 4 daya gudana tsakanin bangarorin biyu.

Sojojin sakan dai sun karyata zargi da ake musu da alaka da kungiyoyin masu tsananin raayi da suka hadar dana alqaeda,kuma sun lashi takobin dawar da doka da order a Somalia,kasar da ta kwashe shekaru 15,babu zaunanniyar gwamnati,wanda hakan ne yasa tuni suka fara kafa kotunan sharia,domin tabbatar dawo da kasar mulkin sharia.

Wannan taron suhu dazai gudana a sudan dai gwamnatocin Yemen dana habasha ne suka dauki nauyin gudanarwa,kasashen da sojojin sakan ke zargi da marawa gwamnatin rikon kwaryan baya.

Ita kuwa gwamnatin rikon dake da matsugunin a garin Baidoa,wanda ke yammacin mogadisho,kuma ke rike da yankuna kalilan na kasar,na zargin cewa ,sojojin sakan islaman na kokarin mulkan kasar baki daya ne.

Rahotannin jamiai dai na nuni dacewa shugaba Yusuf da prime minister Ali mohammed Gedi da kakakin majalisar dokoki Sharif hassan sheikh Adan ,ne zasu jagoranci wakilan bangaren gwamnatin na Somalia.

Majiyar na nuni dacewa Shugaba yusuf yanzu haka yana birnin Nairobi,domin ganawa da jamming diplomasiyyan Amurka akan harkokin Afrika jendayi Frazer,wanda ke yankin gabashin Afrikan domin tattauna yadda lamura ke dada rincabewa a somaliyan.

To sai dai a yau dinne wakilan kungiyoyin musulmi dake rike da mafi yawan sassan somaliyan, suka bar kasar s zuwa wannan taron na sulhu a birnin khartum.Tawagar wadda ta kunshi wakilai 10,ta babar birnin mogadisho ne cikin wani jirgi da kungiyar kasashen larabawan ta aike musu dashi.Tawagar dai ta hadar da Mohammed Ali Ibrahim a matsayin jagora da mataimakin shugaban gamayyar kotunan sharia Sheikh Hussein Mohamud Jumaale,inji shugaban kungiyar sheikh Sharif sheikh Ahmed.

A hirar da yayi da manema labaru,sheikh Ahmed ya bayyana cewa a shirye suke,wajen ganin cewa an samu zaman lafiya a wannan kasa,amma bazasu amince da shirin gwamnati na tura dakarun kiyaye zaman lafiya,domin daidaita somaliyan ba.