1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tattalin arzikin duniya a birnin Davos

January 26, 2006
https://p.dw.com/p/BvAn

A yau aka shiga rana ta biyau na taron tattalin arzikin kasashe na duniya dake gudana a birnin Davos na kasar Swistzerland. Taron wanda ya sami halartar shugabanni da masana tattalin arziki, siyasa da kuma kasuwanci ya yi tsokaci a game da bunkasar tattalin arziki na nahiyar Asia. Batun tattalin arzikin kasashen China da India shi ne yafi daukar hankali a zauren taron.Shugabannin kimanin 2,300 daga kasashe daban daban na duniya ke halartar taron wanda zaá shafe tsawon kwanaki biyar ana gudanar da shi. A jawabin ta yayin bude taron shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta baiyana matakan tada komadar tattalin arziki da sabuwar gwamnatin ta ke da nufin aiwatarwa.