1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Tattaunawa Akan Matsalar Ta'addanci A Nahiyar Turai

May 21, 2004

Tashar DW ta dauki nauyin shirya wani taron bita a hadin guiwa da jaridar General-Anzeiger ta birnin Bonn domin tattauna matsalar ta'addanci a Jamus da sauran sassa na nahiyar Turai

https://p.dw.com/p/BvjO
Tutar Detsche Welle
Tutar Detsche Welle

A lokacin da yake gabatar da jawabi a zauren taron Friedbert Plügler, kakakin ‚yan Christian Union akan manufofin ketare ya ce ita kanta Jamus ba ta tsira daga ayyukan ‚yan ta’adda ba, kamar yadda wasu daga cikin jami’an kasar ke zato kuma a sakamakon haka suke wa barazanar rikon sakainar kashi. Flügler ya kara da cewar:

"Da farko an farfado, amma bayan da kura ta lafa, sai aka sake komawa gigin barci. Abin da ya kamata a fahimta shi ne ita kungiyar nan ta al-ka’ida ba kawai Amurka ko Isra’ila ne ta sanyawa karan tsana ba. Kungiya ce dake kyamar dukkan wadanda ta kira wai kafirai. Abin nufi a nan kuwa shi ne tsarin ci gaban kasashen yammaci. Amma ga alamu, a nan kasar ba a waye da hakan ba."

Wannan maganar gaskiya ce a cewar kwararrun da suka halarci zauren taron. Barazanar tana nan daran-dakau, kuma wajibi ne mahukuntan tsaro da jami’an leken asiri su ba da la’akari da ita sosai da sosai. Amma, bisa sabanin jami’in siyasar, kwararrun sun yi gargadi a game da daukar wani matakin da zai jefa mutane cikin hali na rudami da rashin sanin tabbas da kuma shafa wa dukkan bakin dake nan Jamus kashin kaza. Akwai bukatar daukar matakai na bai daya domin tinkarar matsalar ta ta’addanci, kamar yadda aka ji daga bakin babban editan jaridar General-Anzeiger ta nan birnin Bonn Joachim Westhoff. Ya kuma kara da cewar:

"Bisa ga ra’ayina, muhimmin abu shi ne a rika daukar matakai na wayarwa a kai-akai. Ba za’a iya yada jami’an tsaro domin ba da kariya ga wasu daidaikun gidaje ba. Ita kanta rundunar sojan Jamus ba zata iya daukar wannan nauyi ba."

A hakikanin gaskiya yayata maganar ta’addancin na barazanar mayar da wani bangare na mazauna kasar nan saniyar ware a harkokin rayuwa ta yau da kullum, saboda ana yayata batun ne ba tare da tantancewa ba. Ba shakka akwai wasu masallatai dake yada zazzafar akida ta addini tare da cusa irin wannan ra’ayi a zukatan matasa, wadanda a nasu bangaren suke rungumarsa da hannu biyu-biyu sakamakon halin da suke ciki na zama tamkar saniyar ware, amma fa hukumomin tsaro da na leken asiri sune ke da alhakin bita da kuma nemo hanyoyin magance wannan ci gaba da ake samu. Hare-haren ta’addancin da aka fuskanta a New York, a satumban shekara ta 2001 da kuma watan maris na wannan shekarar a Madrid sun isa zama gargadi a game da muhimmancin hadin kai tsakanin mahukuntan leken asiri na kasa da kasa domin kandagarkin wani sabon harin da ka yi sanadiyyar rayukan wasu dubban mutane nan gaba. Wajibi ne a dauki matakai na wayar da kan jama’a da kuma cike gibin tsaro a duk inda ya kamata, a maimakon gabatar da matakai na ramuwa, wadanda ba sa tsinana kome illa su kara rura wutar matsalar.