1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Toronto a game da cutar AIDS

August 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bumj

A birninToronto na ƙasar canada ƙurrarun massana ta fannin kiwon lahia, na ci gaba da mahaurori, a game da cutar AIDS, albarkacin cikwan shekaru 25, da gano wannan annoba.

Masanan, sun yi na´am da cewa wajibi ne,a ɗauki matakan da su ka dace, da ko wane yanki, na yaƙi da cutar, a maimakon matakan bai ɗaya, da ake anfani da su, ya zuwa yanzu.

Binciken da su ka gudanar ya gano cewa, hanyoyin kamuwa da Sida, sun banbanta, daga wannan yanki zuwa wancen.

A yayin da ya yi bayanni ga manema labarai, shugaban hukumar yaƙi da AIDS, a Majalisar Ɗinkin Dinkin Dunia, Dr Kevin de Cock, ya ce cutar na ci gaba da yaɗuwa kamar wutar daji, a wasu ƙasashen a sakamakon rashin kulla daga magabata.

To saidai duk da haka, an samu ci gaba, ta fannin samar da matakan riga kafi, da kuma rage raddadin cutar da wanda su ka kamu da ita.

Jami´in ya ce, gabacin Afrika, fiye da ko wane sashe, na dunia, ya fi fama da annobar ƙanjamau.

Mahalarta Toronto sun yi tabi da jinjina, ga shahararen mai kuɗin nan ɗan ƙasar Amurika Bill Gates, a sakamakon ƙoƙarin da ya ke, na yaƙi da cutar Sida.