1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tsakanin Gwamnatin Sudan da tsafin yan tawayen SPLM

Yahouza Sadissou MadobiMay 30, 2006

Shugaban ƙasar Sudan Omar El Beshir da mataimakin sa Salva Kiir, sun cimma daidaito a kan batun zaman lahia a kudancin ƙasar

https://p.dw.com/p/Btzv
Hoto: dpa

A cikin daren jiya ne, a ka kawo karshe tantanawa tsakanin gwamnatin Sudan da tsofin yan tawayen kudanci kasar.

Wannan ganawa da ta haɗa tawagar shugaban ƙasa Omar Hasan El Beshir,, da mataimakin sa, Salva Kiir, ta yi bitar inda a ka kwana, a wanzuwar yarjejeniyar zaman lahia, da aka cimma, tsakanin yan tawayen kudancin Sudan, da gwmnati, a watan janairu na shekara ta 2005 a birnin Nairobin ƙasar Kenya.

Wanda a kuma a sakamakon hakan, a kawo ƙarshen yaƙin tsawan shekaru 21, da ya hadasa mutuwar mutane fiye da million 3.

An shirya taron na kwanaki 3 ,bayan da tsofin yan tawayen SPLM,su ka fara zargin gwamnati, da tafiyar haiwainiya, a fannin aikata dukkan ƙuddurorin da yarjejeniyar ta ƙunsa.

Shugaban SPLM, da shugaban ƙasar Sudan, sun ƙara cimma daidaito, na aiki kafaɗa da kafaɗa, domin tabatar da zaman lahia, a kudancin wannan ƙasa.

Omar Hassan El bashir ya sanar manema labarai cewa, akwai babban yauni a kan tsafin yan tawaye da gwamnati na cimma wannan manufa.

To saidai, ɓangarorin 2, ba su cimma matsaya ɗaya ba, a dangane da yankin Abiye, mai arzikin man petur, wanda kuma, ke kan iyaka tsakanin kudu, da arewancin Sudan.

A cikin jawabin da yayi, shugaba Omar El Beshir, ya soki ƙasar Amurika, da ci gaba da ƙargama takukumi ga Sudan, duk da yarjejeniyoyin sulhu da a ka cimma, tsakanin gwamnati da yan tawayen kudanci, da kuma na yankin Darfur.

Ya ce wai kuma,a yanzu, Amurika ta ƙara gitta wani sharaɗi na sai Sudan ta warware rikicin tawaye na gabacin ƙasar.

Ranar 13 ga watan juni mai kamawa, a ke sa ran komawa tebrin shawara tsakanin gwamnatin Sudan, da yan tawayen gabacin ƙasar, a birnin Asmara na ƙasar Erythrea.

Yan tawayen wannan yanki, suma na zargin gwamnatin Khartum, da maiyar da jihohin su saniyar ware.

A nasa ɓangare shugaban SPLM, bugu da ƙari mataimakin shugaban ƙasa Salva Kiir, ya hurta albarkacin bakin sa a game da taƙƙadamar zuwan dakarun Majalisar Ɗinkin Dunia a yanki Darfur.

Ya ce Sudan ba ta ƙi ba,to amma da sharaɗin sai an tantanace ɓallo, ɓallo, iyakokin aikin wannan runduna.

Kuma a cewar sa, gwamnati ta ƙalailaice batun, da wakilin mussamman na Majalisar Ɗinkin Dunia, Lakhadar Brahimi da ya ziyarci Sudan, a makon da ya gabata.