1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron tsaro a Munich

February 14, 2005

A jiya lahadi ne aka kammala taron tsaro cikon na 41 a birnin Munich dake kudancin Jamus

https://p.dw.com/p/Bvd9
Sakatare-janar na MDD Kofi Annan a zauren taron tsaro a Munich
Sakatare-janar na MDD Kofi Annan a zauren taron tsaro a MunichHoto: AP

A lokacin da yake jawabi a zauren taron wanda ya zama tamkar mizanin dangantakar kasashen kungiyar tsaron arewacin tekun atlantika NATO, sakatare-janar Kofi Annan yayi kira a game da kara karfafa hadin kai tsakanin kasashe domin yakar ta’addanci da hana yaduwar miyagun makamai na kare dangi. Wani abin da aka lura da shi a zauren taron shi ne sararawar al’amura a dangantakun Amurka da kawayenta na nahiyar Turai, bayan sabanin da aka sha fama da shi tsakanin sassan biyu sakamakon yakin Iraki. Hatta shi kansa sakataren tsaron Amurka Donalds Rumsfeld, wanda kalamansa kan gurbata yanayin taron na birnin Munich, amma a wannan karon ya nuna halin sanin ya kamata inda ya rika magana da sassautar murya. Mai yiwuwa hakan na da nasaba da kasancewar a wannan karon neman hadin kai ake yi domin ayyukan sake gina kasar Iraki, amma ba neman wasu dalilai na kai mata hari ba. Shi kansa wannan sabani da aka sha fama da shi a zamanin baya ga alamu ya taimaka dukkan sassan suka gane cewar sabanin ra’ayi wajibi ne a tsakanin kawaye kome dangantakarsu, amma idan an yi batu a game da murkushe ta ‚addanci da hana yaduwar miyagun makamai na kare dangi to kuwa tilas ne a samu hadin kai tsakaninsu. Dukkan kasashen Turai da Amurka sun dogara ne da juna a game da manufofin tsaron kai kuma kungiyar NATO na taka muhimmiyar rawa a wannan bangaren, kamar yadda sakamakon taron na birnin Munich ya nunar. A zauren taron shugaban kasar jamus Gerhard Schröder yayi kira a game da sabunwa al’amuran kungiyar, inda ya ba da shawarar nada wata hukuma ta kwararrun da zata zayyana matakan yi wa gamayyar ta tsaro gyaran fuska. To sai dai kuma shawarar tasa ta haifar da sabani a zauren taron saboda gazawar da yayi wajen bayanin tahakikanin abin da yake nufi, inda wasu daha cikin mahalarta taron suka zarge shi da yunkurin rushe kungiyar tsaron ta NATO. A lokacin da yake karin sharhi akan shawarar ta Schröder ministan harkokin wajen Jamus Joschka Fischer yayi nuni da cewar manufa a nan shi ne kirkiro wata hukumnar da zata rika bitar manufofin sadarwa a bangarori da dama tsakanin Amurka da kasashen Turai a baya ga manufofi na soja. Akwai bukatar karfafa hadin kai da daukar matakan tsaro bai daya tsakanin illahirin kasashen kungiyar, musamman a daidai wannan lokacin da aka dinke barakar da ta samu tsakaninsu a zamanin baya. Amma kuma hatta ita kanta hukumar kwararrun da za a nada ba zata iya hana samun sabanin ra’ayoyi tsakanin Amurka da wasu kasashen Turai nan gaba ba, amma kuma a daya bangaren wannan ba zai zama karantsaye wajen bin manufofin tsaro bai daya tsakaninsu ba.