1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron Turai da Afirka a Libya

November 28, 2010

Gwamnatin Libya ta ce shugaban Sudan ba zai halarci taron kyautata hulɗa a tsakanin Turai da Afirka ba

https://p.dw.com/p/QKX2
Shugaba Sarkozy na Faransa yana magana da shugaba Gadhafi yayin taron EU da Afirka a birnin LisbonHoto: AP

Ministan kula da harkokin wajen Libya Moussa Koussa ya sanar da cewar, shugaban ƙasar Sudan Umar al-Bashir baya cikin jerin shugabannin Afirkar da za su halarci taron haɗin gwiwa a tsakanin Tarayyar Turai da kuma Tarayyar Afirkar da zai gudana - farawa daga wannan Litinin ba. A maimakon haka - a cewar ministan, shugaba al-Bashir zai halarci taron kwamitin sulhu da samar da zaman lafiya na ƙungiyar Tarayyar Afirka ne.

Ya ce hukumomin Libya sun buƙaci shugaban na Sudan daya ƙauracewa taron ne saboda barazanar da shugabannin Turai suka yi na janyewa daga taron - idan har ya halarta, inda ministan harkokin wajen Libyar ya ce ƙasar sa ta yi namijin ƙoƙari wajen karɓar baƙuncin taron, kuma ba ta son janyo wani cikas ta hanyar ficewar wasu shugabanni daga zauren taron.

Idan za'a iya tunawa dai kotun ƙasa da ƙasa da ke hukunta masu aikata manyan laifukan yaƙi ne ta bayar da sammacin kame shugaba Umar al-Bashir bisa zargin aikata kissar ƙare dangi a yankin Darfur.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Abdullahi Tanko Bala