1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TARON UN KANN SAMAR DA RUWAN SHA A HABASHA

JAMILU SANIDecember 9, 2003
https://p.dw.com/p/BvnD
A yanzu haka dai daruruwan ministocin ruwa da suka fito daga kasahe dabam dabam na Africa,da kuma wakilan kasahe masu bada taimako hada da masana ilimin kimiya suka halara a baban birnin kasar Habasha tun a jiya litinin, don halartar baban taron majalisar dikin duniya game da samar da ruwan sha mai tsabta a nahiyar Africa da za'a shafe kwanaki shida ana gudanar da shi a kasar Habasha.

Da yake jawabi yayin bude baban taron na majalisar dikin duniya game da samar da ruwan sha mai tsabta a nahiyar Africa,ministan albarkatun ruwan sha na kasar Masar Abu.Zeid ya shaidawa mahalarta wanan taro cewa,kimanin kashi 65 daga cikin dari na alumomin dake zaune a yankunan karkara na nahiyar Africa aka baiyana na fama da matsaloli na karancin ruwan sha mai tsabta,yayin kuma da kashi 73 daga cikin dari na alumomin dake zaune a Africa ba kasafai suke mayar da hankali wajen tsabta ruwan da suke sha ba.

Shi kuwa K.Y. Amako,baban sakataren hukumar habaka tattalin arziki Africa ta majalisar dikin duniya dake karbar bakuncin wanan taro na samar da ruwan mai tsabta a nahiyar Africa,shaidawa mahalarta wanan taro yayi cewa rashin daukar matakan da suka dace wajen alkinta ruwa ya sanya ana cigaba da fuskantar koma baya a fusakar samar da abinci,harkokin kula da lafiya da kuma cigaban masana'antu. Jami'in dai na majalisar dinkin duniya kara da cewa za'a daukar matakan rage matsalolin da ake fuskanta na karancin ruwan sha mai tsabta a tsakanin aluma,ta hanyar samar da ingantatun manufofin da suka dace na tsabta tare kuma da wayar da kann jama'a kann bukatar dake akwai na su tsabta ce muhalin da suke zaune.

Don haka ne Amako ya bukaci alumomin nahiyar Africa,su tarbiyantar da yayan su game da tsabtar jiki data muhali,don kuwa rashin yin hakan na iya sanyawa ayi danasani a nan gaba. Ministan albarkatun ruwa na kasar Masar ya kara da cewa baban kaluban dake gaban kasahen Africa a wanan lokaci da muke ciki shine,gwamnatoci su farka daga barcin da suke yi.

Don haka ne yayi kira ga gwamnatocin nahiyar Africa da kuma kungiyoyi masu zaman kansu na kasahen duniya da su bada tasu gudunmawar wajen yaki da kangin talaucin da ake fama da shi a nahiyar Africa.

Manufar wanan taro dai na majalisar dikin duniya game da samar da ruwan sha a naiyar Africa shine samar wata manufa da gwamnatocin Africa zasu yi amfani da ita,wajen cimma manufar majalisar dikin duniya ta samar da ruwan sha mai tsabta ga nahiyar Africa kafin nan da shekara ta 2015 mai zuwa. Bugu da kari wanan taro dai na majalisar dikin duniya zai tattauna yadda za'a magance matsaloli na talauci a tsakanin kasahen Africa ta hanyar samar da aiyukan yi,tare kuma da bunkasa harkokin zuba jari a aiyukan gona. Hukumar samar da ruwan a Africa ce ta shirya wanan taro da hadin kann majalisar dikin duniya.