1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron wakilan Amurika, EU ,Russia da Majalisar Ɗinkin Dunia a birnin Amman

April 2, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3M

Wakilai ƙungiyar gamayya turai, Amurika, Rasha, da Majalisar Ɗinkin Dunia,sun buɗa zaman taro, yau a birnin Aman na ƙasar Jordan.

Babban ajendar taro, ta shafi halin da ake ciki, a yankin gabas ta tsakiya, da kuma batun tallafi, ga Palestinawa,bayan hawan Hamas bisa karagar mulkin wannan ƙasa.

Idan dai ba a manta ba, Amurika ta yanke hukuncin, katse duk wani tallafi, ga hukumar Palestinawa, muddun Hamas, ba ta yi watsi ba,da aƙidar ta, ta haramta Isra´ila, da kuma kai mata hare haren ta´adanci.

Mahalarta taron, na birnin Amman, na masanyar ra´ayoyi ,a game da mattakan ɗauka, domin tallafawa al´umomin Palestinu, ba tare da wannan tallafi, ya bi ta hannun gwamnatin Hamas ba.

Sakataren harakokin yankin gabas ta tsakiya, na Amurika, David Welch, ya ce Amurika, a shire ta ke, ta ci gaba da kai taimako, ga Palestinu, amma ta hanyar ƙungiyoyin bada agaji, na Majalisar Ɗinkin Dunia.

A nasu ɓangare, ƙasashen larabawa, a sakamakon taron da su ka kammalla ranar laraba da ta wuce a ƙasar Sudan, sun ƙudurci bada taimako, ga Palestinu, duk da kiranye kiranye da Amurika ke yi, na su mayar ga gwamnatin Hamas saniyar ware.