1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron warware rikicin Somalia

September 16, 2010

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta laluɓo hanyar shawo kan rikicin Somalia yayin wani taron da za ta yi a ranar 23 ga Satumba

https://p.dw.com/p/PE7Z
Shugaba Sheikh Sharif Ahmed na SomaliaHoto: ap

Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon zai shirya wani taro na musamman domin tattauna batutuwan da suka shafi Somalia a ranar 23 ga watan Satumba, wanda zai gudana daura da babban taron shekara-shekara da shugabannin ƙasashen duniya daban - daban ke halarta.

A yau Alhamis ne Sabon manzon MDD na musamman zuwa Somalia Augustine Mahiga ya shaida wa kwamitin sulhun majalisar cewa akwai buƙatar duniya ta ƙara yawan sojoji domin tallafawa gwamnatin wucin gadin Somalia dama kuma rundunar ƙungiyar tarayyar Afirka da ke ƙasar.

Mr. Mahiga ya ce ko da shi ke lamura na cigaba da taɓarɓarewa a ƙasar, akwai kyakkyawan fatan inganta sha'anin tsaro da kuma zaman lafiya a ƙasar.

A rahoton sa na baya-bayan nan da ya miƙa wa kwamitin sulhun, babban sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya yi ƙira ga ƙasashe mambobin majalisar da su hanzarta kai ɗaukin sojoji da kuma na kuɗi  zuwa ga gwamnatin na somalia.

Somalia ta daɗe tana fama da rigingimu tun bayan kifar da gwamnatin Shugaba Mohammed Said Barre a shekara ta 199.

Mawallafi: Pinaɗo Abdu

Edita : Ahmad Tijani Lawal