1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron WTO ya watse baran-baram

July 24, 2006
https://p.dw.com/p/BupO

Manyan ƙasashen dunia masu babban kasso, a saye da sayarawa, tsakanin ƙasa da ƙasa,sun kasa cimma daidaito a kan shinfiɗa saban tsarin harakokin hada hadar kasuwanci, tsakanin ƙasashe masu arziki da masu tasowa na dunia.

A taron da su ka gudanar a Geneva, na kasar Suizland, ministocin harakokin kasuwancui na ƙasashen Australiya, Brazil, India, Japon, Amurika da ƙungiyar gamayya turai, sun watse baram baram, a game da wannan batu.

Shugaban hukumar cinaki ta Majalisar Dinkin Dunia, Pascal Lamy, ya bayyana cijewar da aka fuskanta, wajen magance matsalar da tallafi, da ƙasashen masu ƙarfin ttattalin arziki ke baiwa manoman su, abinda ke nakasa manoma na sauran ƙasashen dunia.

Tun shekara ta 2001 a ka fara wannan tantanawa da zumar cimma matakin bai ɗaya, wanda zai tabatar da adalci, a saye da sayarwa, tsakanin ƙasashen dunia.

Nan gaba a yau wakilan za su komawa tebrin shawarwari