1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron 'yan jarida na ƙasa da ƙasa

June 21, 2010

Rawar da 'yan jarida ka iya takawa wajan faɗakar da al'uma akan canjin yanayi shi ne taken taron na bana

https://p.dw.com/p/NzNh
Shugaban Deutsche Erik Bettermann a jawabin buɗe taron Global Media Forum na wannan shekaraHoto: DW

A yau an soma gudanar da Taron yan jarida na ƙasa da kasa akan canji yanayi a nan birnin Bonn.Taron wanda gidan rediyon Dw ya shirya na samun hallarta wakilai na kwararu da yan jarida sama da guda dubu daga ƙasashen duniya daban daban.

Makasudin taron dai shine tattauna butun irin gudunmuwar da yan jarida zasu iya kawo wajan fafutkar da ake yi akan canjin yanayi.da ya ke jawabin bude taron shugaban gidan rediyon Dw Erik Betterman ya yi bayyana cewa duniya dai baza ta rushe ba amma fa za a samun canje canje a ƙayuka da garuruwa da ƙasashe a sakamakon canji yanayi.

Ya ce muna cikin wani hali na ƙalubale wanda ƙasasa guɗa ba zata iya komai sai da sauran ƙasaashe sanan su kansu kafofin sadarwa na da rawar da sukan iya takawa ta hanyar fatatikar da al' uma aka canji yanayi.

Mawallafi:Abdourahamane Hassane

Edita :Abdullahi Tanko Bala