1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron yini uku na yaki da cutar murar tsuntsaye

Zainab A MohammadNovember 9, 2005

Hukumar Who da wasu masana kiwon lafiya sun dukufa wajen samo bakin zaren warware cutar murar tsuntsaye

https://p.dw.com/p/Bu4N
Hoto: AP

Taron kasa da kasa na kwararru ta fannin lafiya a birnin Geneva ,sun zartar da daukan tsauraran matakai na yaki da matsalar zazzabin murar tsuntsaye,wanda zaici kimanin kudi dala billion daya,a kasashe matalauta kadai cikin shekaru 3 masu gabatowa.

Ana bukatar amfani da kimanin dala million 80 cikin gaggawa wa kasashe masu tasowa cikin watanni 6 masu gabatowa,kamar yadda kungiyar samarda da abinci ta mdd ,da kungiyar kula da dabbobi da kuma hukumar kula da lafiya ta mdd suka kiyasta.

Daga cikin wannan adadin kudi dai zaa kebe dala million 60 domin shawo kann yaduwar kwayar cutar da akayiwa lakabi da suna H5N1,a tsakanin kaji da dangoginsu da kuma million 20 a tsakanin mutane.Domin shawo kasn yaduwar zazzabin muran tsuntsaye dake cigaba da yduwa a sassa daban daban na duniya.

Bankin duniyan dai zai bada wadannan tallafin kudaden nen domin taimakawa kasashe matalauta da masu tasowa cikin shekaru 3 masu gabatowa,kasancewar wannan cuta zata fi muni a wadannan kasashen idan ta fara bazuwa.

To sai dai wadannan kudaden basu kunshi na magubngunan da zaa saya domin wadanda suka rigaya suka kamu da cutar ba,da kuma kudaden da zasu kasance na biyabn diyya wa manoman da zasuyi asaran tsuntsayensu na kiwo.

Kakakin Bankin duniya Philipp Hay yace zaa ayi ajiyan wasu kudade ,domin shirin kota kwana,koda yake yayi imanin cewa zaa cimma nasaran dakatar da yaduwar wannan cutar a a gonakin kiwon kaji da dangoginsu dake kasashen kudu maso gabashin Asian.

Taron wanda ya dauki kwanaki 3 yana gudana a birnin Geneva ya samu halartan kwararru da masana harkokin lafiyan mutane da dabbobi kimanin 400.

Bayan kammala wannan taro a yau dai anasaran gudanar da taro na gaba a birnin Beijing din kasar Sin,inda zaayi nazari dangane da matakan da zaabi na kashe wadannan kudade,taron dazai gudana daga 16-18 ga watan Janairu.

A hannu guda kuma bankin raya kasashen Asia ADB ,ayau ta sanar da bada wasu tallafin dala million 300wa kasashen Asia matalauta ,kann dala million 170 na farko data kebewa kasashen domin yakan cutar zazzabin murar tsuntsayen.

Shugaban Bankin Geert van der Linden,yayi karin bayanin cewa kasashe matalauta na bukatar dukkan tallafi da goyon baya na kudi da kwararru na yaki da kwayar cuta