1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tarzuma a ƙasar Gini

October 20, 2010

An shiga halin rashin tabbas kan zagaye na biyu a zaɓen shugaban ƙasar Gini, inda yanzu aka zargi 'yan sanda da nuna ƙarfi da yin fyaɗe

https://p.dw.com/p/PiV5
Dogarawan fadar shugaban ƙasar GiniHoto: AP

A ƙasar Gini 'yan sanda sun buɗe wuta kan masu zanga-zanga inda suka kashe mutum biyu da raunata wasu da dama. Masu zanga zangar dai suna adawa ne da naɗa sabon shugaban hukamar zaɓen ƙasar wanda ɗan ƙabilar abokin hammayan mutumin da suke goyoyn bayan Cellou Dallein Jallo, wanda ke gaba daga cikin 'yan takaran da za su shiga zagaye na biyu a zaɓan ƙasar cikin wannan makon. Ma zauna birnin suka ce anga 'yan sanda na harɓi da harsashen gaske kan matasa. Shugaban ƙungiyar kare haƙƙin bi'adama dake ƙasar Gini Aliyu Brry, yace 'yan sanda sun yi ta shiga lunguna suna harbin mutane, kuma har ta kai suna yi wa mata fyaɗe. Inda Barry yace ɗaukacin birnin Konakry ya kasance a hargitsi. Wani likita da ya nemi a sakaya sunansa, yace aƙalla mutane 29 aka kwatar a asibiti, aksari yara ne, kana akwai ƙananan mata dake cikin waɗanda aka kawo asibitin. Wannan zanga-zangar dai ta zone kwanaki shida kafin zaɓen ƙasar za gaye na biyu, wanda bisa dukkan alamu Cellou Dallein Jallo ya kama hanyar lashewa, domin a zagayen farko ya samu kashi 43 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasiru Awal