1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Iraki gabanin zaben ´yan majalisar dokoki

December 9, 2005
https://p.dw.com/p/BvHI
Ana ci-gaba da kai munanan hare hare a Iraqi kwanaki kalilan gabanin zaben ´yan majalisar dokokin kasar. Kimanin mutane 30 suka rasu sannan wasu dama suka samu raunuka sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai jiya a birnin Bagadaza. Kamar yadda hukumomin kasar suka nunar dan kunar bakin waken ya ta da bam din da ya ke jikinsa a tsakanin fasinjoji dake cikin wata safa. Harin dai na daga cikin munanan hare-haren kunar bakin wake guda biyu a jere da aka kai a Bagadaza cikin kwanaki 3. A ranar talata da ta gabata sama da mutane 40 aka halaka a wani harin kunar bakin wake da aka kai wata kwalejin ´yan sanda. A wani labarin kuma babban sakataren MDD Kofi Annan yayi kira ga ´yan tawaye a Iraqi da su saki dukkan mutanen da suka yi garkuwa da su. Da farko dai wata kungiyar ´yan tawaye ta ce ta kashe wani Ba´amirke da ta yi garkuwa da shi, to amma gwamnatin a Washington ba ta tabbatar da kisan dan kasar mai shekaru 40 da haihuwa ba.