1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Iraki na kara rincabewa

November 26, 2006
https://p.dw.com/p/BuaC

Wasu ´yan bindiga sun yi garkuwa da akalla mutane 21 a lardin Diyala dake arewa da birnin Bagadaza. ´Yan sanda sun ce hakan ya auku ne a garin Kanaan mai nisan kilomita 20 kudu da birnin Baquba wato hedkwatar lardin. A ranar juma´a da ta gabata wasu ´yan bindiga sun yi garkuwa da ´yan shi´a 21 a lardin na Diyala, sannan daga bisani suka halaka su. A dangane da tashe tashen hankulan da suka ki ci suka ki cinyewa a Iraqin, ´yan siyasa na shi´a da sunni sun fara hada kai da juna da nufin kawo karshen mummunan halin da ake ciki. A cikin wani jawabi day ayi ta gidan telebijin mataimakin shugaban kasa Tarek el-Hashemi dan sunni, ya nuna goyon bayansa ga gwamnati karkashin jagorancin dan shi´a FM Nuri al-Maliki. Ita ma kungiyar kasashen musulmi ta duniya ta yi kira ga ´yan shi´a da sunni na Iraqi da su kawo karshen zub da jinin juna da suke yi. A yau ma dai mutum 8 sun rasu a wani harin bam da aka kai a Haswa dake kudu da Bagadaza.