1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Iraki sun halaka akalla mutane 15

December 31, 2005
https://p.dw.com/p/BvEL

Akalla mutane 15 aka kashe sakamakon tashe tashen hankula a Iraqi a yau asabar rana ta karshe a wannan shekara ta 2005. Wani kakakin rundunar sojin kasar ya nunar da cewa an halaka mutane 5 lokacin da wasu da ba´a ganesu ba suka farma wani gidan ´yan suni a Iskandariya. Sannan wasu ´yan sanda 5 sun gamu da ajalinsu a fashewar bam a birnin Bagadaza. Yayin da wani bam da ´yan ta da kayar baya suka dana a kusa da hedkwatar jam´iyar Islamic Party ta Iraqi ya halaka mutum 5 a yankin Al-Chalis. A kuma halin da ake ciki Sudan ta rufe ofishin jakadancin ta a birnin Bagadaza, don ba da kai ga bukatun wasu ´yan bindiga da suka yi garkuwa da ´yan Sudan su 6 ciki har da wani jami´in diplomasiya.