1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankula a Kirkuk dake Iraki

Ibrahim SaniNovember 24, 2007
https://p.dw.com/p/CSjW

Mahukunta a yankin Kirkuk na ƙasar Iraƙi sun kafa dokar ta ɓaci a yankin. Matakin yazo ne a dai dai lokacin da Jami´an tsaron ƙasar ke ƙaddamar da sabbin hare-hare ne, don daƙile fitinar tsageru a yankin. Rahotanni sun ce soji da ´ Yan sanda sama da dubu ɗaya ne ke sintiri, a ciki da wajen birnin na Kirkuk. Janar Jamal Tahir ya ce matakin abune da zai taimaka, wajen inganta harkokin tsaro a yankin baki ɗaya. Yankin Kirkuk dai na ɗaya daga cikin yankuna a Iraƙi dake fuskantar yawaitar tashe- tashen hankula, sakamakon ayyukan tsageru da ´Yan tawaye.