1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Kongo gabanin zabe a ranar lahadi

October 27, 2006
https://p.dw.com/p/BueJ
Kwanaki 3 gabanin zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za´a gudanar a kasar JDK, an kashe mutane 4 a wata musayar wuta da aka yi tsakanin magoya bayan ´yan takaran shugaban kasa biyu wato Josef Kabila da Jean Pierre Bemba. Dukkan sassan biyu da ba sa ga maciji na zargin juna da laifin barkewar fadan a garin Gbadolite dake arewacin kasar a jiya alhamis. Daga cikin wadanda aka kashe a hargitsin kamar yadda wata tashar radiyo ta nunar akwai wani sojin sa kai mai goyon bayan dan adawa Jean-Pierre Bemba.