1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Mogadishu

Hauwa Abubakar AjejeAugust 14, 2007

Ci gaba da kashe yan jarida a rikicin kasar Somalia

https://p.dw.com/p/Btuj
Firimiya Gedi da shugaba Abdullahi Yusuf
Firimiya Gedi da shugaba Abdullahi YusufHoto: AP

fi tashen hankali a duniya,ya fada cikin wannan hali ne tun watan janairu na wannan shekara lokacinda dakarun gwamnatin wucin gadi dana Habasha suka kori magoya bayan kotunan islama da suka tabbatar da doka da oda a birnin a lokacinda suke rike da shi tsawon watanni shida.

Ko da jiya litinin wani bam daya fashe a Mogadishu ya halaka yan sanda hudu da farar hula daya yayinda ake cikin alhinin kashe wasu yan jarida biyu da wasu yan bindiga sukayi a makon daya gabata a birnin na Mogadishu.

Mahad Ahmed Elmi wani fitatccen dan jarida da aka sani da gudanar da shirye shirye da suke suka ga gwamnati da kuma mayakan islama saboda tashe tashen hankula dake ci gaba a kasar,yan bindigar sun harbe shi ne akan hanyarsa ta zuwa aiki yayinda abokin aikinsa Ali Iman Sharmarke aka bindige shi a rana guda a lokacinda yake komawa gida daga janaizar abokinsa.

Sakataren kungiyar yan jarida ta kasar Somalia Omar farouk Osmann yace ana kashe yan jarida ne saboda baiyana ainihin abinda ke faruwa a kasar.

“yan jarida sun zama masu janyo hankalin duniya cewa Mogadishu birnin ne dake cike da hadari,babu zaman lafiya kuma kasar Somalia ta shiga wani mummunan hali fiye da yadda take a baya”

Haka shima shugaban sashen kula da harkokin Afrika a kungiyar yan jarida ta kasa da kasa mai zaman kanta Leonard Vincent,yana da wannan raayi inda yace yan jarida na duniya baki daya suna cikin hadari a kasar Somalia musamman cikin wannan shekara.

“kashe wadannan mutane 2,ya kawo yawan yan jarida da aka kashe zuwa 6 a 2007 a Somalia,hakan kuwa ya sanya kasar ta Somalia ta zama kasa mafi hadari gay an jarida a Afrika cikin wannan shekara”

A halinda ake ciki dai kasar Amurka tayi Allah wadai da kashe yan jaridar tana mai kira ga shugabanin alummomin kasar da na addini da kuma kungiyoyin farar hula da su girmama wadannan mutane biyu ta hanyar ci gaba da sadaukar da kawunansu ga tabbatar da zaman lafiya a Somalia,batu da shima sakataren kungiyar yan jaridar yace yan jarida na kasar su taimaka ga tabbatar da shi.

“akwai bukatar yan jarida na Somalia su kara karfin hali,su sadaukar da kawunansu su kuma kare hakkinsu,su hada aki domin fuskantar wannan kalubale,saboda zaman lafiya na jamaar kasar”

A halinda ake ciki dai yanzu kasashen Afrika karkashin AU sun bukaci komitin sulhu na MDD daya tura dakarunta kwatankacin wadanda tayi niyar turawa zuwa Darfur.

Komitin ya maida martani da bullo da kudirin doka da yayi kira da a duba yiwuwar maye gurnin dakarun AU dana Afrika a Somalia,amma ba tare da yin alkawarin hakan ba.Kodayake yayi alkawarin daukar matakai da bai fayyaye ko wane iri ne ba,akan duk wanda yayi kokarin yin zagon kasa yunkurin wanzar da zaman lafiya a kasar.