1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula a Somalia

Hauwa Abubakar AjejeMay 11, 2006

Mummunan fada na kwanaki 4 a kasar Somalia yayi sanadiyar mutuwar kusan mutane 120,yayinda kungiyoyin adawa suke ci gaba da gwabzawa a birnin Mogadishu.

https://p.dw.com/p/Bu0C
Hoto: AP

Cikin fada na daren jiya kadai mutane 20 sun rasa rayukansu,ciki har da wata mata mai ciki da yaranta 3.

Wannan mummnunan fada dai ya barke net un ranar lahadi tsakanin kungiyoyin isalama da kuma wadanda suke zargi da goyon bayan amurka.

Daruruwan mutane sun samu rauni,cikin wannan fada mafi muni tun fiye da shekaru 10,inda da dama kuma suka tserwa gidajensu dake babban birnin kasar,Mogadishu.

Shugaban wata kungiyar tawaye sayid Muhammad yace,abubuwa sai dada tsananta sukeyi a yankin Siisii,inda aka kashe mutanen 20 a daren jiya.

Yan kungiyoyi dauke da bindiga suna fada da juna ne,a kokarinsu na neman kame babban birnin kasar,bayan rushewar wata yarjejeniya tsakaninsu.

Masu kalailaice alamura sunce,kasar Somalia ta zamo wani fagen yaki tsakanin kungiyoyin Islama da Washington,wadda da dama sukayi imanin cewa tana bada taimakon kudi ga madugan yan tawaye na kasar.

Sayid Muahammad,wanda ke wakiltar kotunan Somalia da suke anfani da dokokin shariar musulunci,domin samarda doka da oda a birnin Mogadishu mai dauke da muatne miliyan 1,yace yan tawayen sun tura yan bindiga kusan 100 cikin Mogadishu domin su yaki jamaar birnin wadanda basa goyon bayansu.

Sai dai wani memba na yan tawayen ya karyata batun,amma ya tabbatar da cewa ana ci gaba da fada a Siisii.

Tuni dai kasar Amurka ta dauki Somalia,wadda babu wata cikakkkiyar gwamnati tun 1991,a matsayin wata maboyar yan taadda.

Babban shehin islamam sheik Dahir Uwais,wanda sunasa ke cikin jerin yan taadda da Amurka take nema,ya zargi Amurkan da laifin goyon bayan madugan yan tawaye domin suyi ramuwar gaiya na kisan sojojin Amurka da akayi a Moagadishu a 1990,lokacinda dakarun majalisar dinkin duniya suka bar yankin cikin kunya.

Masu sa ido na majalisar dinkin duniya,cikin wani rahoto da suka fito da shi jiya laraba,sunce suna bincike game da wata kasa da take karya dokar hana sayarda makamai ta hanyar baiwa yan tawayen kungiyar ARCPC makamai a kasar ta Somalia.

Kodayake jamian na majalisar dinkin duniya basu baiyana ko wace kasa ce ba,amma shugaba mai rikon kwarya na Somalia,Abdullahi Yusuf,yace kasar Amurka ce take goyon bayan yan tawayen.

Amurkan dai ta tabbatar da cewa tana anfani da wannan kungiya wajen zakulo yan taadda da take zaton suna boye a cikin kasar ta Soamlia.