1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankula akan iyakar Chadi da Sudan

December 18, 2005
https://p.dw.com/p/BvFr

Kasar Chadi ta zargi makwabciyarta Sudan da hannu a wani harin da aka kai kan iyakarta da ya halaka sama da mutane 100 sannan wasu 30 suka jikata a garin Adre. Gwamnatin Chadi ta ce ta na da ´yancin fatattakar maharan har cikin kasar Sudan. Kakakin gwamnati a birnin Ndjamena ya ce wasu sojojin ´yan tawaye da suka hada kai da wata sabuwar kungiya da ake kira Rally For Democracy and Liberty RDL suka kai harin. Chadi dai na zargin cewa gwamnatin Sudan na amfani da ´ya´yan kungiyar ta RDL a matsayin sojojin sa kai.