1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rashin aikin matasa na barazana ga Najeriya

Uwais Abubakar Idris
January 23, 2018

Gamayyar kungiyoyin kare hakkin jama’a sun nuna damuwa a kan hatsarin da ke fuskantar Najeriya saboda kashe-kashe da rigingimu gami da koma bayan al’umma da ke tayar da hankali sosai.

https://p.dw.com/p/2rMYa
Nigeria Polizei Polizisten auf Patrouille in Bauchi
Hoto: Getty Images/AFP

 

Kara shiga mawuyacin hali da ake fuskanta a Najeriya kama daga kashe-kashen jama’a da yawaitan garkuwa da mutane a cikin Najeriya da ma rigingimun da ake neman cusa addinini siyasa da kabilanci da sannu a hankali ke naso zuwa wasu kasashen Afirka ne dai suka daga hankalin al'umma Najeriyar.

Nigeria Lagos Benzin
Hoto: dapd

Matsaloli da kalubale da suka ce ana wa saku-saku na zama babbar barazana ga kasar baki daya, musamman  batun hadin kai da dorewar mulkin dimukurdiyyar da ‘yan Najeriyar suka wahala kafin samu a 1999. Mallam Auwal Musa Rafsanjani shi ne shugaban kungiyar Cisilac kuma jami’a a kungiyar kare hakin jama’a ta Tranparrency ya bayyana abinda ke tayara masu da hankali.

Matsalar nan ta cin hanci da rashawa da suka ce duk da kokarin da ake yi har yanzu ba a kai ga ganin hukunta mutanen da ake zargin da aikata ba dai dai ba, musamman sanin cewa Najeriyar na cikin kasashen da ke da hanshakan masu kudi da suka mallaki bilyoyi a dai har mutane 23, kuma duk ma’aikatan gwamnati ne.

Nigeria Polizei Polizisten auf Patrouille in Bauchi
Hoto: Getty Images/AFP

Yayin da kungiyoyin farar hula suka kai ga daga ‘yar yatsa a bayyane take cewa gwamnatin Najeriya tana fuskantar sabon kalubale na shawo kan matsalolin da ake zargin danganta su da siyasa a dai dai lokacin da kasar ke shirin fuskantar babban zabe a shekara mai zuwa.