Tashe tashen hankulla a ƙasar Irak
March 2, 2006Talla
A Irak tashe tashen hankulla na ci gaba da ƙara bazuwa a faɗin ƙasar bakin ɗaya, tun bayan da wasu mutane su ka kai hari, ga ɗaya, daga wuraren ibadar yan ɗarikar Shi´a a ƙarshen watan da ya gabata.
Ya zuwa yanzu, ɗaruruwan mutane, sun rasa rayuka a cikin hare haren ramuwar gayya, tsakanin yan Sunni da yan shi`a.
A sahiyar ƙarin sojoji da jami´an yan sanda fiye da 10 sun kwanta dama a cikin wani harin ta´adanci a arewancin Bagadaza.
A ci gaba kuma da shari´ar tsofan shugaba ƙasa, Saddam Hussain, a karro na farko, ya bayyana cewar, shi ya umurci aikata kissan kiyasun ga mutanen Dujail, da a ka samu da hannu, a cikin kitsa makircin hallaka shi, a yayin da ya kai ziyara a wannan gari, a shekara ta 1982.