1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankulla a ƙasar Irak

February 28, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6Y

Tashe tashen hankulla babu ƙaƙƙabtawa, na ci gaba da hadasa asara rayuka a ƙasar Iraki.

A ranar yau talata, wasu yan ƙunar baƙin wake sun kai tagwayen hare hare a birnin Bagadaza.

Mutane kimanin 30 sun rasa rayuka, sannan da dama sun ji mumuman raunuka.

Bugu da ƙari wani hari makamancin wannan ,ya wakana a tsakiyar kasuwar garin Karrada, wanda shima ya jawo assara rayuka 4.

A ɓanagren sojojin ƙetare , yan ƙasar Britania 2 ,sun sheƙa lahira.

Daga farkon yakin Irai zuwa yanzu, Britania ta yi assara sojoji 103, daga jimmilar sojoji dubu 8, da ta girke a wannan kasa.

A ɗazun nan me kuma, a ka koma shari´ar tsofan shugaban ƙasa Saddam Hussain, tare da muƙaraban sa, su 7, jim kadan, bayan da wasu mutane su ka kai harin da ya yi kaca- kaca, ga ƙabarin ma´aifin Saddam Hussain, da ke Tikirit.

A ɓangasen siyasa kuma, wani rikici ya kunnu tsakanin Shugaban ƙasa Jallal Talabani ,da Praminista Ibrahim Jafari.

Shugaban ƙasar, ya zargi Praminista, da kai ziyara a ƙasar Turquia, ba tare da ya sanar da shi ba.