1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankulla a Fransa

November 2, 2005
https://p.dw.com/p/BvMq

A kasar Fransa rikicin da ya barke a kauyen Kilishi Sous Bois na kussa da birnin Paris, ya fara bazuwa a wasu yankuna na kewayen babban birnin .

A daren jiya masu zanga zangar sun kona a kalla motoci 62 a cikin wata arangama da su ka tada.

Hukumomin yankin Seine Saint Denis, inda rikicin ya faru, sun bayyana daukar mattakai na tabbatar da tsaro da zaman lahia.

A yammancin jiya ,Praminista Dominique de Villepin da Ministan cikin gida Nikolas Sarkozy, sun gana da iyayen matasa 2, da su ka rasa rayuka a Kilishi Sous Bois, wanda kuma sanadiyar wannan mutuwa ne riginginmun su ka faru.

A daya wajen kuma, wani abu mai kama da Bom ya fashe a opishin haraji na birnin Blaye, da ke tazara kilomita 50 da Bordeaux.

A sakamakon wannan yawan tashe tashen hankulla ministan ci kin gida Nikolas Sarkozy ya dage ziyara da zai kaiwa a kasashe Afganistan da Pakistan.