1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe-tashen hankulla a Irak

July 4, 2006
https://p.dw.com/p/Burg

A Irak yan yaƙin sari ka noƙe na ci gaba da kai hare hare a wurare daban-daban na ƙasar.

Harin yau, ya ritsa da mataimakin ministan makamashi , Raad al-Hareth, tare da masu tsaran lahiyar sa 19.

Hare hare ga magabata a ƙasar Irak, sun ƙara ƙamari, duk da saban passalin tsaro da aka tanada.

Hukumomin ƙasar sun jera jami´an tsaro kimanin dubu 50, tare da sojoji dubu 1,7 a birnin Bagadaza.

Ranar asabar da ta wuce, yan takife sun sace wani dan majalisa na ɓangaren sunni, wanda kuma har ya zuwa yanzu babu ɗuriyar sa.

Ita kuwa,rundunar tsaron Amurika ta bada sanarwar bingige wani ɗan ta´ada, da ake zargi da kai harin ranar asabar da ta wuce, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 66.

Sannan ,yan majalisar dokoki, sun yanke shawara kiran Praministan Nuri al Maliki, domin yayi masu ƙarin haske a game da zargin da aka yi wa wani sojan Amurika da yayi wa yarinya fayɗe.