1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashe tashen hankullan kabilanci a birnin Sydne na Australiya

December 13, 2005
https://p.dw.com/p/BvGg

A birnin Sydne na kasar Australiya, rahotani su bayyana kara abkuwar tashe tashen hankulla, masu nassaba da kabilanci.

Wannan ringingimu sun faro, tun ranar lahadi da ta wuce, a yayin da matasa yan assulin kasar ,su ka shirya zanga zangar nuna kin jinnin baki, mussaman larabawa.

A kalla, mutane 30 su ka samu raunuka, da su ka hada da jami´an tsaro.

Domin maida martani, su ma matasa na unguwanin ya ku bayi akasarin su baki ,sun shirya tasu zanga zanga.

Praministan kasar Austaraliya, yayi kira ga al´umma, domin tabatar da zaman lahia.

Ya kuma yi hannun ka mai sanda, ga masu shirin tada zaune tsaye cikin kasa, da cewa gwamnati ta dauki matakan ladabtar da su.

John Haward, ya bayyana hakan , sahiyar yau, a wani taron manema labarai da yayi, jim kadan kamin ya tashi zuwa birnin Kwala lampur, inda zai halarci taron kasashen kudu maso gabancin nahiyar Asia.