1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashi fadin siyasa a Russia

Ibrahim SaniDecember 1, 2007
https://p.dw.com/p/CVWh

Shiryer-shirye sun yi nisa dangane da gudanar da zaɓen ´Yan majalisun dokoki a ƙasar Russia. Jam´iyyu 11 ne ake sa ran za su fafata a zaɓen na gobe lahadi. Zaɓen dake matsayin irinsa na biyar a tsawon shekaru takwas, ana sa ran zai samu halarcin ma su jefa kuri´a miliyan 109. Tuni dai Jam´iyyun adawa na ƙasar su ka zargi fadar Kremlin da ƙoƙarin yin maguɗi, a lokacin wannan zaɓe. Kuri´ar jin ra´ayi ta baya-bayan nan ta nunar da cewa Jam´iyyar URP ta shugaba Putin ce ke a kan gaba dangane da hasashen lashe wannan zaɓe. ´Yan sanda dubu 450 ne ake sa ran za su tabbatar da doka da kuma oda, a lokacin wannan zaɓe dake da matuƙar muhimmanci ga fagen harkokin siyasa a Russia.