1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin hankali a Faransa ya fara lafawa

November 10, 2005
https://p.dw.com/p/BvLe

An fara samun lafawar rashin zaman lafiya da kasar Faransa take Fuskanta a yan kwanakin nan sakamakon zanga zangar da wasu matasa mabiya addinin islama keyi a kasar.

A cewar jamian yan sanda na birnin Faris a yanzu haka yawan motocin da yan zanga zangar ke konewa sun ragu da yawan gaske idan aka kwatanta da abin da ya faru a yan kwanaki kadan da suka gabata.

Ya zuwa yanzu dai tuni ministan harkokin cikin gida na kasar wato Nicolas Sarkozy ya bayar da umarnin tasa keyar duk wani bako da aka samu hannun sa a cikin tayar da zaune tsayen izuwa kasar daya fito.

Bugu da kari Sarkozy ya kara da cewa kusan mutane 120 da aka samu da hannu a cikin wannan rigingimu kusan dukkannin su baki ne daga wasu kasashe na duniya.

Kafin dai zartar da wannan doka sai da ghwamnatin ta faransa ta bayar da umarnin kafa diokar ta baci a wasu gurare a kokarin da take na dakile ci gaban wadan nan rigingimu.